Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al’ummar Nijeriya — Buhari

Share this post on social media

Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al’ummar Nijeriya — Buhari

30729985 1601766849921739 2478333989488836866 n - Maketatan Mutane Ne Suka Talauta Al'ummar Nijeriya — Buhari

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa Maketatan shugabanni suka talauta al’ummar Nijeriya ta hanyar sace arzikin kasa.

Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Birtaniya suka kai masa ziyara a birnin Landon inda ya jaddada cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen maido da Nijeriya kan tafarkin ci gaba idan aka yi la’akari da yanayin da ta karbi mulki daga hannun PDP.

Ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da shirinta na kwato kudaden sata duk da yake ba zai yiwu a gano dukkan kudaden da aka wawure ba inda ya nuna takaicinsa kan yadda aka sace kudaden Nijeriya wanda har sun kasa tsara yadda za su yi rufa-rufa.

Share this post on social media

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You may use these <abbr title="HyperText Markup Language">HTML</abbr> tags and attributes: <a href="" title=""> <abbr title=""> <acronym title=""> <b> <blockquote cite=""> <cite> <code> <del datetime=""> <em> <i> <q cite=""> <s> <strike> <strong>