Boye Kudade A Kasashen Waje Ya Gurgunta Nijeriya — Buhari

Share this post on social media

Boye Kudade A Kasashen Waje Ya Gurgunta Nijeriya — Buhari

30262057 1593534450744979 4548843439879807589 n - Boye Kudade A Kasashen Waje Ya Gurgunta Nijeriya — Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya tsawaita wa’adin shirin garabasar biyan haraji ( VAIDS) zuwa ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2018 inda ya jaddada cewa boye kudade a kasashen waje da kin biyan haraji na gurgunta ci gaban Nijeriya.

Buhari ya ce an tsawaita wa’adin bisa shawarar ma’aikatar kudi kan cewa matakin zai taimaka wajen samun karin kudaden shiga bayan kuma rokon da wasu kungiyoyin kwararru da mutane suka yi bayan wa’adin ya cika a ranar 30 ga watan Maris. Gwamnati dai ta yi barazanar kwace kadarorin duk wanda aka samu da laifin kin biyan haraji.

Share this post on social media

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You may use these <abbr title="HyperText Markup Language">HTML</abbr> tags and attributes: <a href="" title=""> <abbr title=""> <acronym title=""> <b> <blockquote cite=""> <cite> <code> <del datetime=""> <em> <i> <q cite=""> <s> <strike> <strong>